Isa ga babban shafi

Tsohon shugaban kasar Peru Toledo wanda ake zargi ya isa gida bayan an mika shi ga Amurka

Tsohon shugaban kasar Peru Alejandro Toledo ya dawo kasarsa a yau lahadi bayan da aka tasa keyar sa daga Amurka biyo bayan tuhume-tuhumen da ake masa na halasta cin hantsi, rashawa da kuma almundahana a lokacin wa'adinsa.

Lokacin mika tsohon Shugaban kasar Peru  Alejandro Toledo,
Lokacin mika tsohon Shugaban kasar Peru Alejandro Toledo, AFP - HANDOUT
Talla

Dan shekaru 77, tsohon Shugaban da ya rike kasar Peru daga 2001 zuwa 2006, ana zarginsa da karbar haraji daloli daga Odebrecht a bangaren da ya shafi kwangilar gine-gine na Brazil Odebrecht.

Tsohon Shugaban kasar Toledo ya isa Lima daga Los Angeles a hannun jami'an yan sanda na kasa da kasa na Interpol, wadanda suka mika shi ga jami'an tsaro na yankin, kamar yadda hotunan suka nuna.

Shugaban kasar Sudan tare da wasu daga cikin wakilan Gwamnatin sa
Shugaban kasar Sudan tare da wasu daga cikin wakilan Gwamnatin sa REUTERS/Guadalupe Pardo

 

Toledo ya shafe shekaru da yawa yana zaune  kafin ya mika kansa a ranar Juma'a a wata kotun tarayya da ke San Jose, California, inda aka mika shi ga Yan sanda na Marshals ta Amurka.

Za a kai shi gidan yari a Lima, inda ake tsare da sauran masu laifi na kasar da suka hada da Pedro Castillo (2021-22) da Alberto Fujimori (1990-2000).

Ya kamata a ci gaba da tsare shi yayin da yake jiran shari'a nan da watanni 18.

Toledo dai ya musanta zargin da ake yi masa, kuma ya shigar da kara da dama don nuna adawa da tasa keyar sa, wanda Peru ta nema tun a aikin 2018.

Wasu daga cikin magoya bayayan Tsohon Shugaban kasar Vizcara
Wasu daga cikin magoya bayayan Tsohon Shugaban kasar Vizcara AP Photo/Rodrigo Abd

Masu shigar da kara a Peru sun ce suna da wasu mutane biyu da suka ce Toledo ya karbi cin hanci daga Odebrecht.

Kamfanin ya amince da bayar da cin hanci a Brazil da wasu kasashen Latin Amurka da dama a cikin abin da ake kira badakalar wankin mota, al’amarin da ya kia ga kama wasu ’yan siyasa da ’yan kasuwa a gidan yari.

Daya dagta cikin yan kasar da ake tsare da shi,Alberto Fujimori dai yana zaman gidan yari ne saboda laifin cin zarafin dan Adam amma kuma an same shi da laifin cin hanci da rashawa.

Wani tsohon shugaban kasa, Alan Garcia, ya mutu ta hanyar kashe kansa a  2019 yayin da ’yan sanda ke shirin kama shi a shari’ar Odebrecht.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.