Isa ga babban shafi

Macron da Lula sun tabbatar da dawowar alakar Faransa da Brazil

Duk da banbancin da ke tsakanin shugaba Emmanuel Macron da takwaransa Lula da Silva na Brazil, shugabannin biyu sun cimma daidaiton yin tarayya wajen warware tarin matsalolin da Duniya ke fuskanta.

Ganawar shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva da shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Ganawar shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva da shugaban Faransa Emmanuel Macron. © Silvia Izquierdo / AP
Talla

Shugabannin biyu na Faransa da Brazil da ke da banbancin ra’ayi a abubuwa masu alaka da yakin Rasha da Ukraine da kuma rikicin kasuwancin Amurka da China baya ga yakin da Isra’ila ke yi a Gaza, sun amince da yin tarayya wajen tunkarar tarin matsaloli ciki har da dumamar yanayi da kuma kokarin warware matsalolin da ke kunshe cikin yarjejeniyar kasuwancin kudancin Amurka da Turai.

A yammacin jiya Alhamis ne shugaba Emmanuel Macron ya karkare ziyarar da ya ke ta kwanaki 3 a Brazil, wadda ya bayyana da tarba cikin karrama daga takwaransa Luiz Inacio Lula da Silva.

Gabanin karkare taron shugabannin biyu wadanda suka cimma matsaya wajen zuba jarin tsabar kudi euro miliyan 100 don don tunkarar kalubalen matsalar dumamar yanayi, sun kuma sanar da dawowar alaka tsakanin kasashen biyu wadda a baya ta gamu da tangarda musamman a lokacin mulkin shuga Jair Bolsonaro da ya rika sukar maidakin Macron.

Shugaba Lula ya bayyana sabuwar alakar Brazil da Faransa a matsayin wadda za ta amfani kudancin Amurka baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.