Isa ga babban shafi

Sojojin Brazil sun yi wa gwamnati gagarumar sata

Rundunar soojin Brazil ta sanar da killace sojoji akalla 160 a barikinsu domin gudanar da bincike a kan bacewar wasu manyan bindigogi masu sarrafa kansu guda 21, cikin su har da wadanda kan iya kakkabo jirgin sama. 

Wasu sojojin Brazil
Wasu sojojin Brazil REUTERS/Ricardo Moraes
Talla

Sanarwar sojin ta ce binciken ya shafi yadda wadannan bindigogi guda 13 kirar ’50-caliber’ da wasu guda 8 samfurin ‘7.62-caliber’ da suka bace a ranar 10 ga wannan wata, daga rumbun ajiye makaman da ke garin Barueri mai nisan kilomita 25 daga birnin Sao Paulo. 

Shugabannin sojin sun bayyana fargabar fadawar makaman a hannun kungiyoyin da ke aikata laifuffuka a kasar da ta yi kaurin suna wajen fafatawar da ake yi tsakanin jami’an tsaro da kungiyoyin da ke dauke da makamai. 

Masana sun ce bindigogin kirar 7.62-caliber na da nauyin kilo 4 da rabi, kuma na iya harba harsasai 700 a cikin minti guda, yayin da samfurin 50-caliber ke da nauyin kilo 58, kuma yana iya kakkabo jirgin sama kai tsaye. 

Bacewar wadannan makamai shi ne mafi girma da aka taba gani a tarihin sojin Brazil, kamar yadda cibiyar yaki da tashe tashen hankular dake Sou da Paz ta sanar. 

Rundunar sojin kasar da farko ta fara tsare sojoji 480 da suka yi aiki a barikin a ranar da makaman suka bata, amma daga bisani sai aka sallami sauran bayan mako guda, inda aka rike 160. 

Sakataren Tsaron Sao Paulo, Guilherme Derrite ya ce akwai barazana sosai muddin wadannan makamai suka fada hannun kungiyoyin dake aikata laifuffuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.