Isa ga babban shafi

An kashe shugabar al'ummar bakar fata a Brazil

‘Yan bindiga sun harbe wata shugabar al’ummar bakar fata a arewa maso gabashin Brazil da ta shahara wajen yaki da wariyar launin fata, lamarin da ya jawo suka daga masu fafutuka da hukumomin gwamnati.

Maria ta jima tana fafutukar kare bakaken fata a kasar ta Brazil.
Maria ta jima tana fafutukar kare bakaken fata a kasar ta Brazil. © AFP
Talla

Maria Bernadete Pacifico, shugabar kungiyar quilombos a Brazil, wato kungiyar da bayi bakar fata suka kafa ta mutu bayan da wasu mutane biyu sanye da hular babur suka bindige ta, kusa da birnin Salvador na jihar Bahia.

Matar wadda aka fi sani da Mama Bernadete, 'yar shekaru 72, ita ce babbar wakiliya a majalisar quilombos ta Brazil (CONAQ), kuma tsohuwar ministar daidaiton launin fata na birnin Simoes Filho da ke arewa maso gabashin kasar.

Ta kuma yi fafutuka don ganin an yi adalci a kan kisan danta, Flavio Gabriel Pacifico dos Santos, wani shugaban al'umma wanda aka kashe shekaru shida da suka gabata.

Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva wanda ya bayyana alhininsa da damuwa game da kisan nata, ya ce ma'aikatunsa na daidaiton launin fata da na kare hakkin bil'adama sun aike da wakilai domin gudanar da bincike.

A nata bangaren ma'aikatar mata ta yi Allah wadai da kisan gillar a cikin wata sanarwa da ta fitar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.