Isa ga babban shafi
Italiya - Brazil

Italiya ta bayar da sammacin kamo mata Robinho

Ma'aikatar shari'a ta Italiya ta bayar da sammacin kama tsohon dan wasan Brazil Robinho, bayan da babbar kotun kasar ta tabbatar da samunsa da aikata laifin fyade.

Robinho.
Robinho. AFP PHOTO/ ROSLAN RAHMAN
Talla

Ma'aikatar ta bukaci taimakon hukumar 'yan sandan duniya ta Interpol domin kamo mata tsohon tauraron kwallon kafar.

Robinho, wanda cikakken sunansa shi ne Robson de Souza, yana zaune ne yanzu haka a Brazil, kasar da dokokinta ba su amince ta mika ‘yan kasarta zuwa ga wata ba bisa zargi ko tuhumar aikata laifuka, wanda hakan ke nufin Robinho zai fuskanci kama shi ne kawai idan ya yi balaguro zuwa kasashen waje.

Tsohon dan wasan kasar Brazil Robinho.
Tsohon dan wasan kasar Brazil Robinho. Elcio Ramalho/ RFI

A shekarar 2017, wata kotu a birnin Milan ta samu Robinho da wasu 'yan kasar Brazil guda biyar da laifin yi wa wata mata fyade bayan dirka mata barasa a wani wurin shakatawa.

Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin a shekarar 2020, inda kuma kotun kolin Italiya ta tabbatar da shi a watan da ya gabata.

Sai dai Robinho, mai shekaru 38, ya sha musanta zargin.

Ya buga wa Brazil wasa sau 100, zalika ya taka leda a wasu manyan kungiyoyin Turai da suka hada da Real Madrid da Manchester City da kuma AC Milan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.