Isa ga babban shafi
Brazil

An kama matashin dake kutse asusun ajiyar bankin Neymar a Brazil

‘Yan sandan Brazil sun sanar da kama wani matashi mai kimanin shekaru 20 da suka yi imanin cewa yana kutsawa asusun bankin dan wasan kwallon kafar kasar Neymar Junior yana wawure kudade sannu a hankali, inda ya sace jummular sama da dala dubu 40.

Dan wasan Brazil da PSG Neymar.
Dan wasan Brazil da PSG Neymar. NELSON ALMEIDA AFP
Talla

‘Yan sanda a Sao Paulo sun ce wanda ake zargin ya yi kutse ne a wani banki da ba a bayyana sunansa ba inda dan wasan Paris St-Germain (PSG) da Brazil da mahaifinsa kuma manajan ke da asusu.

Ko da yake rundunar ‘yan sandan ba ta bayyana sunan dan wasan ba a cikin sanarwar, amma wani jami’in da ke kula da lamarin ya ce Neymar ne.

Shidai wannan matashi ya kware a harkar kusten tare shiga asusun ajiyar fitattun mutane, inda yakan zare Kannan kudi ta yadda baza ayi saurin ganewa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.