Isa ga babban shafi

Ana fargabar fuskantar zafi a bana mafi tsanani a tarihi

Majalisar dinkin duniya ta ce shekarar da ta gabata itace mafi zafi da duniya ta gani, sai dai ta yi gargadin cewa 2024 zata fi bara muni.

Tsananin zafin na faruwa ne saboda sauyin yanayi
Tsananin zafin na faruwa ne saboda sauyin yanayi AP - Edmar Barros
Talla

A bara an sami rahoton narkewar kankara a guraren da ba’a saba gani ba, da kuma fari a sassan duniya, yayin da koguna suka kafe, ruwan tekuna kuma suka ja baya.

A wani rahoton shekara-shekara da hukumar ta fitar, ta ce dukannin binciken da ta gudanar ya nuna cewa 2023 itace mafi zafi a tarihin duniya.

Rahoton binciken ya kuma ce shekaru biyun da suka gabata, sune mafi tsananin zafi cikin shekaru 10 da suka gabata, yayin da ake fargabar zafin zai ci gaba da tsananta a bana.

Ko da yake karin haske shugaban hukumar kula da yanayi ta majalisar dinkin duniya, Chief Omar Boddour ya ce har yanzu babu wani mataki da kasashe ko kuma hukumomin da ke da ruwa da tsaki suke dauka don shawo kan matsalar dumamar yanayi.

Ko da yake mayar martani babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Gutterres ya ce wannan bincike ya nuna irin hadarin da duniya ke tunkara.

Hukumar wadda ke kula da yanayi ta ce a bara na sami karuwar zafi a tantagaryar kasa da kaso 1.45 kan ma’aunin zafi yayin da aka sami karuwar zafi a karkashin ruwa da kaso 1.5 akan ma’aunin zafi, abinda ya dara wanda aka gani a 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.