Isa ga babban shafi

An rufe makarantu a Sudan ta Kudu saboda yanayi na matsanancin zafi

Yanayi na matsanancin zafi ya tilasta wa mahukuntan Sudan ta Kudu rufe makarantu a fadin kasar don kauce wa irin hadarrin da ke tattare da yanayin, duba da yadda ya ke ci gaba da ta'azzara..

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir.
Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir. AP - Gregorio Borgia
Talla

Bayanai sun ce masana yanayi sun tabbatar da cewa nan da makonni masu zuwa kasar za ta tsinci kanta cikin tsananin zafin da bata taba ganin irin sa a tarihi ba.

Ma’aikatar Ilimi da ta lafiya sun yi hadin gwiwa wajen shawartar iyaye da su yawaita zubawa yaran su ruwa ajiki tare da killace su a gida ba tare da barinsu shiga rana ba.

Gwamnatin kasar ta yi barazanar karbe lasisin duk makarantar da aka samu a bude lokacin wannan tsananin zafi, sai dai kuma bata yi karin haske kan lokacin da za’a bude makarantun ba.

Masana yanayi sun alakantan tsananin zafin da karancin ruwan sama, sauyin yanayi da kuma fari da kasar ke fama da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.