Isa ga babban shafi

Hukumar Lafiyar Ghana ta yi gargadi kan sauyin yanayi

Hukumar Lafiya ta kasar Ghana ta bayyana fargaba dangane irin sauyin yanayin da kasar ke ciki, saboda haka, ta jaddada bukatar kara wayar da kan al’umma.

Hoto don misali.
Hoto don misali. © MURTADHA RIDHA / AFP
Talla

Cikin wata takadar jawabi da Hukumar ta fitar, ta shawarci al’ummar kasar musamman masu fama da matsalar Asama da ma duk wani rashin lafiya da ke da alaka da numfashi, da su yi takatsantsan game da hatsarin da lafiyarsu ke ciki a wannan lokaci, duba da irin gurbataccen iskar da take kadawa dauke da kura, wanda hakan ka iya tada musu larurar da suke dauke da ita.

Ita ma hukumar kula da yanayi ta kasar ta yi gargadi da cewa, yanayin zai iya ta’zzara fiye da yadda yake yanzu, daga watan Maris mai kamawa zuwa Afrilu.

Daga cikin matakan kariya da hukumar ta bayar, an shawarci masu irin wadannan larura musamman yara da tsofaffi da su takaita duk wani abin da zai fitar da su waje, sannan su yawaita amfani da takunkumin hanci domin kare kansu daga shakar kura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.