Isa ga babban shafi
ZANGA-ZANGA

Gwamnatin Indiya ta nemi tattaunawa da fusatattun manoman kasar

Jami’an ‘yan sanda a India sun  yi amfani da hayaki mai sanya hawaye da kuma ruwan zafi kan dandazon manoman da ke tattaki da nufin isa New Delhi fadar gwamnatin kasar a kokarinsu na kalubalantar matakin gwamnati kan kayyade farashin kayakin da suke noma tun gabanin girbi.

Yadda manoma suka nufi New Delhi, babban birnin Indiya a cikin manyan motoci, ranar 13 ga Fabrairu, 2024, a zanga-zangar neman gwamnati ta sassauta musu tsadar hatsi.
Yadda manoma suka nufi New Delhi, babban birnin Indiya a cikin manyan motoci, ranar 13 ga Fabrairu, 2024, a zanga-zangar neman gwamnati ta sassauta musu tsadar hatsi. AP - Rajesh Sachar
Talla

Manoman wadanda galibinsu suka fito daga jihar Punjab ta arewacin kasar sun shafe tsawon lokaci suna tababa da gwamnatin kasar kan dokar da ta kayyade farashin kayakinsu, lamarin da ya kaisu ga maka gwamnati gaban kotu.

Ana dai kallon dambarwar ta Manoma da gwamnatin India a matsayin batun da ka iya kawo tarnaki ga takarar Firaminista Narendra Modi da ke neman tazarce a zaben kasar na watan Mayu.

Shugaban kungiyar manoman, Sarwan Singh Pandher, ya shaidawa manema labarai cewa za su tsagaita zanga-zangar tasu tsawon kwanaki biyu, inda za su dora daga inda suka tsaya ranar Juma’a, har sai gwamnati ta basu tabbaci kan farashin hatsi.

Ministan noma na kasar, Arjun Munda, ya wallafa a shafinsa na X cewa, gwamnati a shirye ta tattauna da manoman kasar kan yadda za a samar musu da mafita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.