Isa ga babban shafi
India

Dubban Manoma a India sun gudanar da zanga-zanga

A kasar India dubunnan manoma sun yi zanga -zanga a kusa da babban birnin New Delhi a wannan Lahadi, inda suka sha alwashin ci gaba da bijirewa gwamnati kan dokokin aikin noma da ake cece kuce da suke ganin za su lalata rayuwarsu.

Yadda manoma suka gudanar da zanga-zanga a kasar India 05/09/21.
Yadda manoma suka gudanar da zanga-zanga a kasar India 05/09/21. Money SHARMA AFP
Talla

Masu zanga-zangar da suka kunshi Maza da Mata sunyi ta rera taken "manoma, Leburori da kuma haɗin kai!", dauke da tutocin ƙungiyar manoma ta ƙasa a gundumar Muzaffarnagar ta jihar Uttar Pradesh.

Manoma sun yi sansani a kan iyakokin Delhi tun daga ƙarshen watan Nuwamba lamarin da ke zama cikin manyan ƙalubalen gwamnatin Firayminista Narendra Modi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.