Isa ga babban shafi

Adadin mutanen da wutar dajin Chile ta kashe ya karu zuwa 112

Alkaluman mutanen da wutar dajin Chile ta hallaka ya kai 112 dai dai lokacin da jami’an kashe gobara ke ci gaba da aikin dauki don dakile bazuwar wutar wadda ta yi gagarumar illa musamman a yankunan tsaunuka.

Wutar dajin ke matsayin ibtila'i mafi muni da Chile ta gani bayan girgizar kasar shekarar 2010.
Wutar dajin ke matsayin ibtila'i mafi muni da Chile ta gani bayan girgizar kasar shekarar 2010. AP - Andres Pina
Talla

Har zuwa yanzu ana ci gaba da laluben wasu daruruwan mutane da suka bace a wutar dajin, lamarin da ya sanya fargabar yiwuwar karuwar adadin mutanen da ibtila’in ya kashe.

Shugaba Gabriel Boric ya bayyana wutar dajin a matsayin mafi muni da kasar ta fuskanta kwatankwacin girgizar kasar shekarar 2010 da ta kashe daruruwan mutane.

Hukumar kashe gobara ta Chile ta ce yanzu haka akwai tarin gawarwaki a yankunan tsaunuka wadanda zafin wutar ya hana iya isa garesu.

Rahotanni sun ce wutar dajin ta kone ilahirin gidajen yankunan da ke kan tsaunukan lamarin da ya hallaka mutane da dama da basu kai ga fita daga gidajensu da wuri ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.