Isa ga babban shafi

Adadin wanda wutar daji ta kashe a Algeria ya karu zuwa 38

Ma’aikatar cikin gida a Algeria ta tabbatar da mutuwar mutane 38 a wutar dajin da ta afkawa yankin arewacin kasar inda bayanan ke cewa akwai daruruwan wadanda suka jikkata koda ya ke suna samun agajin gaggawa a asibitocin kasar.

Yankin arewacin Algeria mai fama da ibtila'in wutar daji.
Yankin arewacin Algeria mai fama da ibtila'in wutar daji. AFP - FADEL SENNA
Talla

Ministan harkokin cikin gida na Algeria Kamel Beldjoud ya ce mutane 24 suka mutu a yankin El Tarf da ke kan iyakar kasar da Tunisia yayinda wasu mutum biyu Uwa da ‘Ya suka mutu a yankin Setif.

Rahotanni sun ce tuni aka kwashe iyalai 350 daga El Tarf tare da tsugunar da su a wasu yankuna, inda a bangare guda kuma jami’an agaji ke ci gaba da kokarin kashe wutar.

A cewar rahotannin masu aikin kashe gobarar na amfani da jiragen shalkwafta ne don ganin sun yi nasarar kashe wutar dajin wadda zuwa yanzu ta fantsama yankuna 16 a cikin dajin na El Tarf.

Hukumar kare rayukan jama’a ta Algeria ta ce wutar dajin ta wannan karon ita ce mafi muni da kasar ta gani a tarihi.

Zuwa yanzu dai wutar dajin ta kone tarin gidaje a kauyukan da ke tsakanin dazukan na Tarf.

Arewacin Algeria na fama da matsalar wutar daji duk shekara inda ko a bara ta kashe mutane 90 tare da da kone kadada fiye da dubu 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.