Hukumomin Chile sun ayyana dokar ta baci domin yaki da gobarar daji a yankunan masu yawon bude ido
A wannan Asabar, jami’an kwana-kwana na ci gaba da gudanar da ayyukan agaji a kasar Chile inda aka ayyana dokar ta baci a jiya domin yaki da munanan gobarar dazuzzukan da ke bazuwa a yankunan masu yawon bude ido na kasar ta Latin Amurka. Akala mutane kusan 10 ne suka mutu.
Wallafawa ranar:
Gobarar da ta afkawa kasar ta jefa yankin nan da aka sani da wurin shakatawar Vina del Mar da ke tsakiyar kasar a gabar tekun Pacific, a yankin Valparaiso cikin gajimaren hayaki; suna barazana ga ɗaruruwan gidaje, banda haka tilastawa mutane da dama kaura daga gidajen su .
Jami’an kashe gobara na ci gaba da aiki tukuru don murkushe gobarar wacce ke kokarin yaduwa ga gidajen da kusa da wurin.
A garuruwan Estrella da Navidad, masu tazarar kilomita 200 kudu maso yammacin babban birnin kasar, gobarar da ba a shawo kanta ba ta kone kusan gidaje talatin, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin tserewa zuwa wannan yanki da ke kusa da wurin shakatawa na Pichilemu.
A yankin Valparaiso kadai, gobarar ta lakume sama da hekta 7,000, a cewar CONAF, ofishin kula da gandun daji na kasar Chile.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu