Isa ga babban shafi

Kasashen latin Amurka na son shirya gasar kofin kwallon kafar duniya a 2030

Kasashen Argentina da Chile da Uruguay da Paraguay sun gabatar da aniyarsu ta hadin guiwa a hukumance domin neman izinin karbar bakwancin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2030. 

Kofin gasar kwallon kafa ta duniya
Kofin gasar kwallon kafa ta duniya © AFP - LUIS ROBAYO
Talla

Wato gasar ta shekarar 2030, za ta kunshi wani al’amari na musamman ganin cewa, a wannan lokacin ne za  acika shekaru 100 cur da aka fara gudanar da gasar ta cin kofin duniya a tarihi a can filin wasa na Montevideo da ke kasar Uruguay. 

A ranar Talata ne, kasashen uku suka gabatar da aniyar tasu, inda shugaban Hukumar Kwalllon Kafa ta Kasashen Kudancin Amurka, Alejandro Dominguez ya  bayyana kwarin guiwar cewa, hukumar kwalloon kafa ta duniya FIFA za ta amince da bukatarsu. 

Sai dai fa, akwai kasashen Spain da Portugal da Ukraine da su ma ke neman tikitin daukar nauyin gasar.kuma ana ganin Hukumar Kwallon Kafa ta nahiyar Tura za ta mara musu baya tukuru. 

Kazalika akwai Saudiya da ita ke nazarin yin hadin guiwa da Masar da Girka wajen daukar nauyin gasar tac in kofin duniya a 2030. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.