Colombia ta dawo da jakadanta gida biyo bayan wasu kalaman shugaban Argentina
A jiya Juma'a ne kasar Colombia ta sanar da kiran jakadanta a Argentina domin tattaunawa, bayan da shugaban kasar Argentina Javier Milei ya bayyana shugaban kasar Colombia Gustavo Petro a matsayin dan gurguzu mai kisa.
Wallafawa ranar:
Shugaban Argentina Javier Milei a wata hira da wani dan jarida dan Colombia ya dangata shugaban Colombia Gustavo Petro a matsayin "mai kisa, dan gurguzu wanda ke zubar da kimar Colombia".
Nan take Shugaban na Colombia Gustavo Petro ya mayar da martani ga kalaman takwaransa na Argentina, inda ya bayyana cewa wadanda suka kai masa hari "ba su da masaniyar menene tsarin gurguzu", ya kara da cewa "mun yi imani kuma muna son cewa hanyoyin samar da kayayyaki suna hannun jama'a da kuma yadda ake gudanar da ayyukansu.
Kasar ta Colombia ba tare da jan kaf aba,ta kira jakadanta a Argentina, Camilo Romero, "don tuntuba", in ji ma'aikatar harkokin wajen kasar a Bogota.
Dangantaka tsakanin Colombia da Argentina a tarihi tana da kyau, amma ta tabarbare tun lokacin da Javier Milei ya hau kan karagar mulki a watan Disamba 2023.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu