Shugaba Petro na Colombia ya bada sanarwar kama dansa
Shugaban kasar Colombia, Gustavo Petro, ya sanar a yau asabar cewa, an kama babban dansa Nicolas Petro, da ake zarginsa da halasta kudaden haram, da kuma mallaka arziki ba bisa ka'ida ba, dangane da wata badakala da ke da alaka da yakin neman zaben shugaban kasar.
Wallafawa ranar:
Shugaba bangaren hagu na farko a Colombia ya wallafa sakon ne a shafinsa na Twitter.
Wasu rahotanni na nuni cewa ana zargin matar da karbar makudan kudade daga masu safarar miyagun kwayoyi a shekarar 2022, a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa Gustavo Petro.
Yan lokuta bayan zabensa a matsayin shugaban kasar, Gustavo Petro na fuskantar matsaloli da dama wajen ganin an amince da sauye-sauyensa a majalisar dokoki, ko ma a cikin babban shirinsa na "cikakken zaman lafiya" da kungiyoyin masu dauke da makamai.
Shugaba Gustavo Petro ya yi wa gwamnatinsa garambawul ne a karshen watan Afrilu, yayin da kawancensa a majalisar dokoki da masu ra’ayin rikau da masu sassaucin ra’ayi suka watse.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu