Isa ga babban shafi
KWALON KAFA

Mutumen da ya lashewa Brazil kofunan kwallon kafa na duniya har sau 4, Mário Zagallo ya mutu yana dan shekaru 92.

ya kasance dan wasan kwallon kafa daya tak,  da ya taba sabe kofunan kwalayen kafar duniya har sau 4, kafin  zama mai horarawa, Mário Zagallo ya Mutu a ranar juma'a ya na dan shekaru 92 a duniya, ya kuma Mutu ya bar katafaren gado ga duniyar  kwallon kafa.

Mário Zagallo a lokacin wasan karshe na gasar cin kofin duniya na  1998 da aka buga tsakanin Brésil da  Fransa a filin wasan   Stade de France,  12 yuli 1998.
Mário Zagallo a lokacin wasan karshe na gasar cin kofin duniya na 1998 da aka buga tsakanin Brésil da Fransa a filin wasan Stade de France, 12 yuli 1998. © AFP / GABRIEL BOUYS
Talla

 

Mutumen da ake yi wa lakabi da Prof ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarori 4 daga cikin 5 da Barazil ta Samu wajen sabe kofunan gara kwallon kafar duniya da ta yi.

Ya kuma zama dan wasan kwallon kaf ana farko a  duniya ya sabe cofunan duniya a matsayinsa na dan wassa, haka kuma da lokacin da ya ke mai horarwa.

Ya dai sabe kofunan ne sau biyu a lokacin da yake buga wasa, tare da Pelé a 1958 a kasar Suède da kuma 1962 a Chili, haka kuma a matsayinsa na mai horarwa ya safe kofin 1970 a Mexico da kuma a 1994 a kasar Amurka.

Sau daya ya taba yin rashin nasarar kasa sabe kofin na duniya a 1998  bayan da Bulolin kasar Faransa suka yi wa barazil ci 3-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.