Isa ga babban shafi

An gudanar da jana’izar mutane da suka rasa ransu sanadiyar harin bom din Iran

Gwamnatin Iran ta gudanar da jana’izar mutane 85 da harin tagwayen Bam ya hallaka kwanaki uku da suka gabata, wanda kuma tuni kungiyar IS ta dauki nauyin kaishi. 

Yadda aka gudanar da Jana'izar mutanen da suka rasa ransu a Iran.
Yadda aka gudanar da Jana'izar mutanen da suka rasa ransu a Iran. AFP - -
Talla

 

Mutanen da aka yi jana’izarsu a yau din sun hadar da maza 41 sai mata da kananan yara 44, cikin su kuma fiye da 12 ‘yan asalin kasar Afghanistan ne. 

Bayanai sun ce an gudanar da jana’izar ne a babban masallacin birnin Kerman, inda nan ne aka gudanar da jana’izar babban kwamandan kasar Qaseem Sulaimani da Amurka ta hallaka shekaru 4 da suka gabata. 

Shugaban kasar Ebrahim Raisi ya halarci taron jana’izar daga nan kuma ya kai ziyara kabarin na Qaseem  Soulaimani. 

Kamfanin Dillancin Labaran kasar Tasnim ya ruwaito cewa an yiwa mamatan kebantaciyar jana’izar da ta kunshi iyalansu kadai, tare da binne su a kebantaciyar makabarta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.