Isa ga babban shafi

IS ta dauki alhakin kashe mutane 100 a Iran

Kungiyar IS ta dauki alhakin kaddamar da harin tagwayen bamaa-bamai da ya kashe kimanin mutane 100 a wurin taron tunawa da babban kwamandan sojin Iran, Qassem Soleimani wanda jirgin Amurka mara matuki ya kashe shi a Iraqi a shekarar 2020.

People stay next to destroyed cars after an explosion in Kerman, Iran, Wednesday, Jan. 3, 2024. Iran says bomb blasts at an event honoring a prominent Iranian general slain in a U.S. airstrike in 2020
IS ta dauki alhakin harin Kerman a Iran AP
Talla

A cikin wata sanarwa da wallafa a shafin Telegram, kungiyar ta IS te ce, mayakanta ne suka tayar da bama-baman da suka yi damara da su a cikin dandazon jama'ar da suka hallara a makabartar da aka binne Soleimani da ke birnin Kerman a ranar Laraba.

Tagwayen hare-haren sun kuma raunata mutane 284 da suka hada da mata da kananan yara.

Za mu yi zazzafar ramuwa kan wadanda suka kai harin ta hanyar amfani da sojojin Soleimani. Inji Mohammad Mokhber, mataimaki na farko na shugaban kasar Iran.

Tun da farko, wata majiya ta shaida wa Kamfanin Dillacin Labaran Gwamnatin Kasar IRNA cewa, wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam din farko a wurin taron tunawa da Soleimani wanda aka kashe shekaru hudu da suka gabata.

Majiyar ta ce, ga alama shi ma bam na biyu ya tashi ne bayan wani dan kunar bakin waken ya sake tayar da shi.

Tuni Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi tur da wanna harin da ya bayyana a matsayin na matsoratan 'yan ta'adda a Kerman, yana mai mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma gwamnatin kasar.

Kafar talabiji ta kasar ta nuna hotunan dandazon Iraniyawa a sassan biranen kasar suna rera wake-waken, inda suke cewa " Mutuwa ta tabbata ga Isra'ila". "Mutuwa ta tabbata ga Amurka".

Hukumomin Iran sun bukaci gudanar da gagarumar zanga-zanga a kasar a wannan Juma'ar, lokacin da za a yi jana'izar mutanen da suka mutu a harin tagwayen bama-baman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.