Isa ga babban shafi

An kashe sama da mutane 100 a wani harin bam a Iran

Sama da mutane 100 ne suka rasa rayukansu a wani harin tagwayen bama-bamai da aka kaddamar kan jama'ar da suka yi dandazo a Iran domin tunawa da marigayi Janar Qassem Soleimani da Amurka ta kashe shi a wani harin jirgi mara matuki.

Wurin taron da aka kai harin tagwayen bama-bamai da suka kashe sama da mutane 100 a Iran
Wurin taron da aka kai harin tagwayen bama-bamai da suka kashe sama da mutane 100 a Iran AP - Mahdi Karbakhsh Ravari
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zaman dari-dari a yankin Gabas ta Tsakiya sakamakon yakin Isra'ila da Hamas a Zirin Gaza.

Harin na wannan Larabar ya auku ne a kusa da kabarin marigayin da ya kasance shugaban da ke kula da ayyukan dakarun juyin-juya-halin Iran a Masallacin Saheb al-Zaman da ke birnin Kerman a yankin kudancin kasar.

Tuni matakimakin gwamnan Lardin Kerman, Rahman Jalali ya bayyana wannan harin a matsayin na ta'addanci.

Shekaru hudu kenan da mutuwar Soleimani wanda harin na jirgin Amurka mara matuki ya kashe shi a birnin Bagdad na Iraq.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da farmakin kan jama'ar na Iran.

Kodayake Isra'ila ta kai jerin hare-hare kan wasu daidaikun mutane a Iran saboda shirin nukiliyar kasar, amma ba ta taba kai hari kan taron jama'a ba.

Kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi irinsu IS sun sha kaddamar da hare-hare a baya da suka yi sanadiyar mutuwar fararen hula a yankin da mabiya akidar Shi'a ke da rinjaye a Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.