Isa ga babban shafi

Iran ta rataye wasu mutane 4 da ke yiwa Isra'ila aikin leken asiri

Iran ta rataye wasu mutane 4 da kotu ta samu da laifin yiwa Isra’ila aikin leken asiri hukuncin da ke zuwa kasa da makwanni 2 bayan zartas da makamancinsa kan wani mutum da shima aka same shi da laifin na leken asiri a cikin kasar.

Iran ce kan gaba a sahun kasashen da ke aiwatar da hukuncin kisa bayan China.
Iran ce kan gaba a sahun kasashen da ke aiwatar da hukuncin kisa bayan China. AFP
Talla

Da safiyar yau Juma’a ne mahukuntan na Iran suka rataye mutanen 4 mambobin wata kungiyar ‘yan zagon kasa mai alaka da yahudawa a yankin arewa maso yammacin kasar da ke gab da iyakar Azerbaijan daga yammaci.

Ma’aikatar shari’ar Iran da kanta ta wallafa batun aiwatar da hukuncin ratayar a shafinta na Mizan, mutanen da ta bayyana sunansu da Vafa Hanareh da Aram Omari da kuma Rahman Parhazo sai mace guda Nasim Namazi wadanda dukkaninsu aka samesu da laifin aiki da sashen leken asirin Isra’ila Mosad.

Shafin na Mizan ya ce mutanen 4 sun kaddamar da yaki ne kan addinin Allah ta hanyar hada kai da Yahudawa haka zalika sun kalubalanci tsaron kasa da kuma cin amanar kasar.

Har zuwa yanzu dai Iran ba ta amince da zaman Isra’ila kasa ba, dalilin da ya sanya bangarorin biyu takun-saka a batutuwa da dama tsawon shekaru.

Ko a ranar 16 ga watan Disamba sai da aka rataye wani mutum guda a lardin Sistan-Baluchistan na Iran bayan samunsa da yiwa Isra’ilan leken asiri, kari kan wasu mutum 4 a watan Disamban bara.

Kungiyar Amnesty International ta sanya Iran a matsayin kasa mafi zartas da hukuncin kisa bayan China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.