Isa ga babban shafi

Yadda kasashen duniya suka rike kadarorin Rasha

Bayan da shugaba Vladimir Putin ya aike da sojoji zuwa Ukraine a shekarar 2022, Amurka da kawayenta sun haramta mu'amala da babban bankin kasar Rasha da ma'aikatar kudi, tare da rike kusan dala biliyan 300 na kadarorin Rasha da ke ajiye a kasashen Yamma.

Shugaban Rasha Vladmir Putin kenan
Shugaban Rasha Vladmir Putin kenan via REUTERS - SPUTNIK
Talla

Amurka ta ba da shawarar cewa, ya kamata kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 su binciko hanyoyin da za a bi wajen kwace wadannan kudade, a cewar jaridar Financial Times.

Wadannan kadarorin, a ina suke kuma menene Rasha za ta iya yi idan an kwace su?

Vladimir Putin lokacin wani jawabi a taron manema labarai da ya gabatar a birnin Moscow, ranar 19 ga Disamba, 2019.
Vladimir Putin lokacin wani jawabi a taron manema labarai da ya gabatar a birnin Moscow, ranar 19 ga Disamba, 2019. AP - Pavel Golovkin

Asusun ajiyar rarar kudade

Kamar sauran manyan bankunan kasashe, babban bankin Rasha ya sanya wasu kudaden ajiyarsa da kuma zinare a cikin manyan bankunan kasa da kasa, kuma kimanin rabin wadannan kadarori an adana su ne a manyan bankunan Yammaci.

Babban bankin kasar ya tabbatar da cewa an kulle asusun ajiyar kasar mai dauke da kadarori kimanin dala biliyan 300 a kasashen yammacin duniya.

Jimillar kudaden waje da kuma zinare mallakar Rasha sun kai dala biliyan 612 a lokacin da aka rufe su.

Putin ya zargi kasashen Yamma da kaddamar da yakin tattalin arziki a kan Rasha, inda ya bayyana matakin rufe asusun ajiyar kasarsa a matsayin yunkurin handame kadarorin kasar.

Shugaban Rasha, Vladmir Putin (Hagu) tare da shugaban Amurka, Joe Biden, yayin wata ganawa da suka yi a Geneva, Switzerland, ranar 16 ga Yuni, 2021.
Shugaban Rasha, Vladmir Putin (Hagu) tare da shugaban Amurka, Joe Biden, yayin wata ganawa da suka yi a Geneva, Switzerland, ranar 16 ga Yuni, 2021. © AP / Alexander Zemlianichenko

Masu rajin kishin kasa sun soki gwamnan babban bankin kasar, Elvira Nabiullina kan yadda ta bari aka rufe asusun ajiyar da ke dauke da irin wannan adadi mai yawa.

Da me da me aka rikewa Rasha ne?

Babban bankin Rasha bai ba da cikakken bayani game da adadin da aka rufe amma ana iya samun cikakken bayani daga takaddun adana bayanai game da abin da Rasha ta mallaka daga farkon shekarar 2022.

A wancan lokacin, babban bankin kasar Rasha ya mallaki kadarorin biliyan 207 na kudin Euro, da dalar Amurka biliyan 67, da kuma biliyan 37 na kudin fam din Birtaniya.

Shugabar babban bankin Rasha, Elvira Nabiullina kenan, yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a birnin Moscow a watan Oktoba, 2023.
Shugabar babban bankin Rasha, Elvira Nabiullina kenan, yayin wani taron manema labarai da ta gudanar a birnin Moscow a watan Oktoba, 2023. AP

Har ila yau, kasar tana da hannun jarin da ya kunshi dala biliyan 36 na yen, kudin Japan, biliyan 19 na dalar Canada, dala biliyan 6 na kudin Australiya da dala biliyan 1.8 na kudin Singapore, sai kuma hannun jarin kasar na Swiss franc da ya tasamma kusan dala biliyan guda.

Babban bankin kasar Rasha, ya ce wadannan kadarorin anyi amfani da su ne wajen sanya hannun jari a asusun ajiyar kasashen waje, da kuma asusun kamfanoni masu zaman kansu

Yaya aka yi da dukiyar Rasha?

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelesky daga tsakiya, tare bda shugabannin kasashen G7 a Hiroshima na kasar Japan.
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelesky daga tsakiya, tare bda shugabannin kasashen G7 a Hiroshima na kasar Japan. AP - Stefan Rousseau

Babban bankin kasar Rasha baya boye wadanda suke da hannayen jari, don haka tantance kadarorin da kasar ta mallaka ba zai kasance abu mai wahala ba.

Yawancin kadarorin da suka hada da na 'yan asalin kasar Rasha da kamfanoni masu zaman kansu da suka fito daga kasar, an garkame asusun ajiyarssu na kasashen waje.

Kwace ko kuma ramuwar gayya?

Rasha ta ce itama za ta amfani da irin matakan da kasashen Yamma suka dauka a kanta, wajen rike kadarorinsu.

“Wani babban jami'in Rasha ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters bisa sharadin sakaya sunansa cewa, "Kare dukiyoyin sirri abu ne mai muhimmanci, musamman ga wadanda suka shafe shekaru aru-aru suna ciyar da kasar."

Masana tattalin arzziki a Rasha, sun ba da shawarar cewa idan aka kwace kadarorin Rasha to kadarorin masu zuba jari na kasashen waje da ke makale a wasu asusun na musamman na iya fuskantar barazana, don haka ya kamata gwamnatin kasar ta dauki matakan da suka dace.

Ba a fayyace ainihin adadin kudin da ke cikin wadannan asusun ba amma hukumomin Rasha sun ce, sun tasamma dala biliyan 300 da aka rike wa kasar.

Mai magana da yawun faddar gwamnatin Kremlin, Dmitry Peskov kenan, lokacin da yake ganawa da 'yan jarida a birnin Moscow.
Mai magana da yawun faddar gwamnatin Kremlin, Dmitry Peskov kenan, lokacin da yake ganawa da 'yan jarida a birnin Moscow. AP - Alexander Zemlianichenko

Kakakin gwamnatin Kremlin, ya shaidawa manema labarai a makon jiya cewa Rasha za ta kalubalanci duk wasu matakan rike mata kaddarori da aka yi mata a kotu.

"Idan aka kwace mana wani abu, za mu duba abin da za mu kwace muma," in ji Peskov.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.