Isa ga babban shafi

Kasashe 193 sun kada kuri'a kan kudirin bukatar tsagaita wuta a Gaza

Kasashe 193 sun kada kuri’a a zauren Majalisar Dinkin Duniya kan kudirin da ke neman tsagaita wutar dindindin da nufin kawo karshen hare-haren da Isra’ila ke kaiwa yankin Gaza, wanna na zuwa a dai dai lokacin da Alkaluman Falasdinawan da Isra’ila ta kashe ke kaiwa dubu 18.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. AFP - YUKI IWAMURA
Talla

Wannan zaman kada kuri’a da aka karkare a cikin daren Talata wayewar yau Laraba, ya samu amincewar kasashe 153 yayinda wasu 10 suka  kalubalance shi ciki har da Amurka da Isra’ila sai kuma wasu 23 da suka kauracewa zaman.

Jakadun Saudiya da Masar a zauren Majalisar sun godewa kasashen da suka kada kuri’ar goyon bayan tsagaita wutar a Gaza, inda suka ce zaman ya nuna yadda kasashen Duniya ke goyon bayan kawo karshen zubar da jinin Falasdinawa.

Zuwa yanzu dai fiye da 80 na al’ummar gaza miliyan 2 da dubu 300 sun rasa matsugunansu, kuma kaso mai yawa na wadanda aka kashe mata ne da kananan yara sai tarin jami’an kiwon lafiya da ‘yan jaridu.

Bayan rashin nasarar makamancin zaman a juma’ar makon jiya wanda Amurka ta hau kujerar naki tare da goyon bayan ci gaba da zubar da jinin Falasdinawa a yankin na Gaza, Sakatare Janar na Majalisar Antonio Guterres ya yi amfani da sashe na 99 wanda ya bashi damar amfani da kujerarsa don gargadin barazanar yakin ga zaman lafiyar duniya, kundin da rabon ayi amfani da shi tun a shekarar 1971.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.