Isa ga babban shafi
RIKICIN SUDAN

Har yanzu Amurka da saudiyya sun gaza kawo karshen rikicin Sudan

An gaza samar da ci gaba a tattaunawar kawo karshen rikicin Sudan da Saudiyya da Amurka suka kasance masu shiga tsakani, yayin da rashin jituwa tsakanin manyan hafsoshin sojin kasar biyu ta haifar da kalubale ga ayyukan jin kai a kasar.

Shugaban gwamnatin sojin Sudan, Janar Abdel-Fattah Burhan kenan, lokacin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida a birnin New York ranar 22 ga Satumba, 2022.
Shugaban gwamnatin sojin Sudan, Janar Abdel-Fattah Burhan kenan, lokacin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida a birnin New York ranar 22 ga Satumba, 2022. AP - Aron Ranen
Talla

Rashin ci gaba a tattaunawar da ke faruwa a birnin Jedda, ya rushe fatan da mutum sama da miliyan shida da rabi a ciki da wajen kasar ke yi, abin da ya kara haifar da tabarbarewar tattalin arziki da kuma rikicin kabilanci a Darfur.

Yayin da rundunar sojin Sudan din ta ce ta kwace ikon babban birnin kasar, Khartoum, dakarun kai daukin gaggawa na RSf kuma sun fadada ayyulan ne a yankuna Darfur da kuma Kordofan.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, masu shiga tsakani a shirye suke a ci gaba da tattaunawar neman mafita.

A ranar Litinin ne, gwamnatin Amurka ta sanya takunkumi kan wasu manyan jami’an tsaro biyu da suka yi aiki karkashin tsohuwar gwamnatin Omar El-Bashir, sakamakon zarginsu da hannu wajen rura rikicin Sudan.

A ranar Asabar din makon jiya ne, Janar Abdel Fattah al-Burhan ya shaidawa wani taron soji da aka gudanar cewa, wannan yak iba zai kare ba, har sai gwamnati ta kwato dukkanin yankunan kasar da ke hannun ‘yan tawaye.

Yanazu haka dai, rundunar RSF ta sake bude kasuwanni da asibitoci tare da tura ‘yan sanda aiki a sassan Darfur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.