An saki 'yan jarida uku da aka yi garkuwa da su a kudancin Mexico
A Mexico, ofishin mai gabatar da kara a jihar Guerrero dake Kudanci ta sanar da sako wasu 'yan jarida uku da aka yi garkuwa da su, a wannan yanki da ake fama da tashe tashen hankula.
Wallafawa ranar:
Yan jaridar da suka hada da Silvia Nayssa Arce, Alberto Sánchez da Marco Antonio Toledo, masu gabatar da kara sun kuma tabbatar da sakin Guadalupe Denova, matar daya daga cikin ‘yan jaridar da aka sako, Marco Antonio Toledo.
An sace Marco Antonio Toledo, darektan El Espectador na mako-mako na gida kuma wakilin kafofin yada labarai da yawa, a ranar 19 ga Nuwamba a Taxco. An yi garkuwa da sauran 'yan jaridar biyu, Arce da Sánchez, daga kafafen yada labarai na yanar gizo RedSiete, a ranar 22 ga watan Nuwamba a cikin wannan birni.
Ana ɗaukar Mexico a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe mafi haɗari a duniya ga 'yan jarida, a cewar ƙungiyar yan jaridu ta kasa da kasa (RSF).
A ranar 16 ga Nuwamba, an harbe dan jarida mai daukar hoto Ismael Villagómez Tapia, mai ba da gudummawa ga jaridar kasar El Heraldo de Juárez a Ciudad Juarez da ke arewacin Mexico, kan iyaka da Amurka. An kama mutane uku da ke da hannu a wannan kisan gilla.
Akalla wasu ‘yan jarida biyar ne aka kashe a Mexico tun farkon wannan shekara, a cewar ƙungiyar yan jaridu ta kasa da kasa.
Fiye da 'yan jarida 150 ne aka kashe a kasar tun shekara ta 2000 kuma 28 ba a gansu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu