Isa ga babban shafi

Akalla rayukan mutane 29 sun salwanta a wani hadarin motar safa a kasar Mexico

 Akalla fasinjojin 29 ne suka rasa rayukansu wasu 19 kuma suka jikkata sakamakon fadawar da wata motar safa ta yi  cikin  wani rame a wani yanki mai tsaunuka dake jihar Oaxaca a kudancin kasar Mexico, kamar yadda mai shigar da karar yankin ya sanar.

kwararu masu neman kasusuwan mutane a wani rame, dake cikin jihar Jalisco, a kasar Mexico  31 mai.
kwararu masu neman kasusuwan mutane a wani rame, dake cikin jihar Jalisco, a kasar Mexico 31 mai. AFP - ULISES RUIZ
Talla

Mai shigar da karar yankin da hadarin ya faru Bernardo Rodriguez Alamilla, ya sanar da cewa, daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sun hada ne da mata 15, biyu daga cikinsu kuma sun cika ne a lokacin da ake yi masu magani a asibiti, a yayin da 13 suka kasance maza da suka hada da karamin yaro guda.

Kamar yadda rahoton yan sanda ya nunar,  Motar safar malakar wani kamfanin sufurin yankin,  na kan hanyar zangon karshe ne,  bayan da amarecen jiya ta fito daga birnin Mexico zuwa garin  Santiago de Yosondua mai kunshe da kimanin mutane dubu 15.

Hatsarin ya faru ne a cikin yankin Magdalena Peñasco mai kunshe da mutane akalla dubu 3.500, daya daga cikin yankuna da tsaunuka suka killace, da kuma ke amfani da motocin safa, wajen gudanar da tafiye tafiye.

Bahasin farko da mai shigar da kara ya bayar kan dalilin faruwar hadarin, ya nuna cewa, mai yi yiwa ne motar ta kubucewa dirban motar safar  ne, da ya kaita ga fadawa ramen mai zurfin mita 25.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.