Isa ga babban shafi

Wakilan kasashen duniya 175 sun fara taron takaita illar sharar robobi

Afirka – Wakilan kasashen duniya 175 yanzu haka suka yi gangami a Nairobi dake kasar Kenya, inda ake saran su samar da wata yarjejeniyar da zata shawo kan matsalar robobin da ake zubarwa wadanda ke gurbata muhalli.

Lokacin da shugaban Kenya William Ruto ke bude taron dake gudana a karkashin Majalisar dinkin duniya yau a Nairobi
Lokacin da shugaban Kenya William Ruto ke bude taron dake gudana a karkashin Majalisar dinkin duniya yau a Nairobi AFP - SIMON MAINA
Talla

A shekarar da ta gabata ne wadannan kasashe a karkashin Majalisar dinkin duniya suka fara mahawara a kan yadda za’a magance wannan matsalar ta zubar da robobi wadanda ke toshe magudanan ruwa da mamaye tafkuna da kuma tekuna suna gurbata muhalli, tare da yin illa ga mutane da dabbobi tare da sauran hallitu.

Rahotanni sun ce yayin da kasashe da dama suka amince da matakan da ake shirin dauka, akwai ra’ayoyi daban daban a kan irin matakan da suka dace a dauka domin samar da maslaha.

Wurin da ake sake sarrafa sharar robobi a Saint-Marie-La-Blanche dake kasar Faransa
Wurin da ake sake sarrafa sharar robobi a Saint-Marie-La-Blanche dake kasar Faransa AFP - JEFF PACHOUD

Yayin bude taron na yau a birnin Nairobi, shugaban taron ‘dan kasar Peru, Gustavo Meza-Cuadra ya yi gargadin cewar gurbata muhallin da robobin ke yi na matukar barazana ga muhallin jama’a da lafiyar Bil Adama da kuma duniya baki daya.

Bayanai sun ce wakilai sun gana sau biyu kafin wannan taron na yau, wanda za’a kwashe mako guda ana yi, domin nazari a kan daftarin da aka tsara tun daga watan Satumba.

Akalla kasashe 60 suka bukaci daukar matakai masu tsauri domin rage mu’amala da kuma yin robobin wadanda ake amfani da sinadaran man fetur wajen sarrafa su, matakin da ya samu goyan bayan kungiyoyin kare muhalli daban daban.

Amma wannan matsayi bai samu amincewar wasu daga cikin kasashen dake samun makudan kudade wajen kera robobin ba, cikin su harda Amurka, wadda ta dade tana bukatar amfani da hanyar sake sarrafa su ta wasu hanyoyi na daban, maimakon takaita amfani da su.

Yadda sharar robobin ke yiwa tekuna illa
Yadda sharar robobin ke yiwa tekuna illa AP - Ben Curtis

Daftarin dai ya duba bangarori da dama mahalarta wannan taro a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya zasu duba domin daukar matsayin da zai ceto duniya daga wannan matsalar.

Wakilai sama da 2,000 ke halartar taron, cikin su harda wadanda ke fafutukar ganin ba’a haramta amfani da robobin baki daya ba, abinda ke nuna cewar mahawara za tayi zafi tsakanin mahalarta wannan taro.

Daruruwan masu rajin kare muhalli dauke da allunan dake da rubuce rubucen da suka hada da, ‘’matsalar robobi = matsalar sauyin yanayi’’ suka gudanar da zanga zangar lumana a karshen mako a birnin Nairobi, domin zaburar da mahalarta taron wajen ganin sun dauki matakin rage yawan robobin da kamfanoni ke sarrafawa.

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya bayyana gurbata muhallin da robobi keyi a matsayin abinda ke yiwa rayuwar bil Adama illa, inda ya yi kiran sauyin tunanin bil Adama akan yadda ake amfani da su da kuma yadda ake zubar da shararsu a kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.