Isa ga babban shafi

Sai mun lalata hanyoyin karkashin kasa da Hamas ta gina - Isra'ila

Dakarun Isra'ila da ke fagen daga a zirin Gaza, sun ce mataki na gaba da su ke son dauka a yakin da suke yi da Hamas, shi ne nemo wa tare kuma da lalata manyan hanyoyin karkashin kasa da mayakan Hamas su ka samar a yankin, wadanda suke amfani da su.

Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant a lokacin da ya ziyarci wani sansanin sojojin kasar da ke yaki a Gaza.
Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant a lokacin da ya ziyarci wani sansanin sojojin kasar da ke yaki a Gaza. REUTERS - RONEN ZVULUN
Talla

Ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant, ya ce babban kudirin da kasar ta sa a gaba shine lalata mayakan Hamas a Gaza da kayayyakinsu da kwamandojinsu da dakunan ajiyarsu da kuma na sadarwa.

Babban mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila Rear Admiral Daniel Hagari ya bayyana cewa, dakarun sojin kasar na amfani da ababen fashewa wajen lalata hanyoyin karkashin kasa da Hamas ta gina, wanda ya ke da nisan kilomita da dama a Gaza.

Tankokin yakin Isra’ila na fuskantan turjiya daga mayakan Hamas da ke amfani da hanyoyin karkashin kasa wajen yi musu kwanton bauna.

‘Yan kasar Isra’ila sun bayyana fargabarsu kan hare-haren da sojojin kasar ke kaiwa wanda ka iya kara jefa mutanen da aka yi garkuwa da su cikin hadari, wadanda ake kyautata zaton ana tsare da su a cikin ramukan da ke karkashin kasa, sai dai Isra'ila ta ce ba za ta amince da butun tsagaita bude wuta ba har sai an sako mutanen.

Tun bayan da mayakan Hamas suka kai hari cikin Isra’ila, da yayi sanadiyar mutuwar mutane dubu 1 da dari 4 tare da yin garkuwa da wasu 240 a ranar 7 ga watan Oktoban daya gaba, Isra'ila ta fara luguden wuta a Gaza ta sama tare da amfani da sojojin kasa, wanda ya lallaka Falasdinawa sama da dubu 10 da dari 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.