Isa ga babban shafi

An cika wata daya da fara rikicin Hamas da Isra'ila a Gaza

Wata guda bayan bayan fara gwabza rikicin Hamas da Isra’ila, fara ministan Isra’ila Benjamin Natanyahu ya sha alwashin ganin kasarsa ta amshe ragamar tsaron Gaza da ta ke yiwa uwan bama-baman, wanda ma’aikatar lafiyar Falasdinu ta tabbatar da mutuwar mutane sama da dubu 10.

Yau ake cika wata daya da faro rikicin Hamas da Isra'ila.
Yau ake cika wata daya da faro rikicin Hamas da Isra'ila. REUTERS - AHMED ZAKOT
Talla

A ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata ne, Hamas ta kai hari cikin Isra’ila da yayi sanadiyar mutuwar mutane dubu 1 da dari 4 aka sarinsu fararen hula, sannan ta yi garkuwa da wasu sama da dari 240 ciki harda yara da tsofaffi.

Isra’ila na shan suka daga wajen kasashen duniya game da yadda ta ke gudanar da al’amuran yakin Gaza, inda ma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce Gaza ta zama makabartar yara.

Sama da mutane miliyan daya da dubu dari 5 ne suka bar gidajensu a Gaza, inda su ke neman mafaka a wasu yankunansa, ga kuma matsalar kai agaji da ake fuskanta.

Amma Netanyahu ya bayyana cewa za su ci gaba da yakin har sai Isra'ila ta maido da cikakken tsaro a yankin Gaza.

"Lokacin da babu tsaro a hannunmu, abin da zai faru shi ne farmakin Hamas wanda ba za mu iya kwatanta shi ba."

Kalaman na Netanyahu na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amurka ke cewar shugaba Joe Biden ya tattauna da shugaban na Isra’ila ta waya kan batun ba da damar kai kayan agaji, duk da ya ke babu wata yarjejeniya da suka cimma.

Sai dai yayin da kasashen duniya da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya ke butar a tsagaita wuta a rikin, babbar kawar Isra’ila Amurka a na ta bangaren neman bada damar isar kayan agaji ne kawai ta ke yi.

A makon da ya gabata, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da ya kammata zirayar yankin Gabas ta Tsakiya a yau Talata, ya bada shawarar hukumomin Falasdinawa su amshi ragamar jagorancin Gaza daga hannun Hamas bayan kammala yakin, lamarin da Hamas ta ce ba za ta aminta da shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.