Isa ga babban shafi

Gungun G7 zai fidda matsayarsa kan yakin Isra'ila da Hamas

Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7, za su cimma matsaya ta bai daya a laraban nan, game da yakin Isra'ila da Hamas a Gaza da ya lakume rayukan Falasdinawa sama da dubu 10, da kuma wasu kusan dubu daya da dari 4 a bangaren Isra’ila.

Ministocin harkokin wajen kasashen G7, a lokacin ganawarsu a Japan.
Ministocin harkokin wajen kasashen G7, a lokacin ganawarsu a Japan. AP - Eugene Hoshiko
Talla

Ana sa ran ministocin a cikin sanarwar hadin gwiwar da za su fitar, su yi kiran dakatar da rikicin don samun damar gudanar da ayyukan jin kai a Gaza.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, wanda ya isa Japan domin halartar taron bayan kamala ziyarar da yayi a yankin Gabas ta Tsakiya, ya bukaci kungiyar ta G7 ta yi magana da murya daya kan rikicin.

Ministan harkokin wajen Japan da ke karbar bakuncin taron, Yoko Kamiwaka ta ce akwai bukatar ministocin kasashen wajen G7 su yi kira ga kasashen da abin ya shafa da su dakatar da rikicin don samun damar kai agaji, lamarin da ake gani a matsayin matakin farko na ci gaba da ba da kai agaji yankin.

“Akwai hadin kai bisa la'akari da halin da ake ciki na bukatar agajin gaggawa a Gaza, ana bukatar a gaggauta fadada ayyukan jin kai ga fararen hular Falasdinu”.

Isra’ila dai na ci gaba da ruwan bama-bamai a Gaza, tun bayan harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan daya gabata, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutanen ta dubu daya da dari 4.

Sai dai ma’aikatar lafiyar Gaza ta ce hare-haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa sama da dubu 10 da dari 3.

Fara ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya bayyana cewar babu batun tsagaita wuta da kuma kai man fetur yankin Gaza, har sai Hamas ta sako mata mutanenta sama da dari 240 da take rike dasu.

Haka nan ya sha alwashin ganin kasarsa ta ci gaba da rike ikon yankin bayan yakin, matakin da tuni Amurka ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajen ta Vedant Patel ta yi adawa da shi.

"Matsayinmu shi ne a baiwa Falasdinawa hakkinsu wajen yanke wannan hukunci kuma Gaza kasa ce ta Falasdinu kuma za ta ci gaba da zama kasar Falasdinu, "gaskiyar magana, ba ma goyon bayan sake mamaye Gaza, haka ma Isra'ila ba ta goyon bayanta.”

Abinda kasashe suka maida hankali akai a yanzu dai shine samar da mafita ga wannan rikici da ke ci gaba da lakume rayukan fararen hula mafi yawancinsu yara da mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.