Isa ga babban shafi
RIKICIN GAZA

Duk wanda ya taba Isra'ila, zai gamu da fushin Amurka - Blinken

Kasar Amurka ta ce duk wata kasar da ta kuskura tace zata taimakawa kungiyar Hamas domin yaki da Isra’ila zata dandana kudarta, domin Amurka zata ci gaba da bai wa kasar Yahudun duk wani taimako da take bukata domin kare kanta. 

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken kenan, tare da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken kenan, tare da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. via REUTERS - POOL
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya sanar da haka bayan ganawar sirri da suka yi da Firaminista Benjamin Netanyahu a ziyarar da yanzu haka ya kai Isra’ilar domin jaddada goyan bayan kasar a yakin da take gwabzawa da kungiyar Hamas. 

Blinken yace a matsayinsa na Sakataren harkokin wajen Amurka da kuma Bayahude ya ziyarci kasar ne domin nunawa duniya cewar Amurka na tare da Israila a koda yaushe, kuma zasu ci gaba da bai wa kasar kayan yaki duk da sanin cewar tana da karfin kare kan ta. 

Sakataren yace babu dalilin kaddamar da hare haren da kungiyar Hamas ta yi da kuma hallaka fararen hula manya da kanana, saboda haka zasu ci gaba da baiwa kasar Israila makamai, yayin da tuni wasu suka isa kasar. 

Blinken ya sake gargadi ga duk wata kasa ko kungiyar dake tunanin amfani da wannan dama domin kaiwa Israila hari cewar, kada ta kuskura, domin kuwa Amurka na goyan bayan Israilar. 

Shiga alamar sauti, domin sauraron rahoton Khamis Saleh.

 

01:38

Rahoton Khamis Saleh

A na shi jawabi, Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya bukaci duniya ta tashi tsaye wajen murkushe kungiyar Hamas kamar yadda aka yiwa kungiyar IS. 

Netanyahu yace babu wani banbanci tsakanin kungiyoyin biyu, lura da yadda take kai hari tana kashe yara da mata wadanda basu ji, basu gani ba. 

Firaministan wanda ya bayyana Hamas a matsayin mai adawa da ci gaban zamani, ya yabawa ziyarar Blinken a matsayin jaddada goyan bayan su ga Yahudawa. 

A karshe Netanyahu ya bukaci murkushe Hamas da kuma hana duk wata mu’amala da ita tare da hukunta duk wata kasa ko kungiyar da ta ci gaba da hulda da kungiyar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.