Isa ga babban shafi

'Yar fafutukar yaki da sanya Hijabi a Iran ta lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya

Narges Mohammadi ta lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel yau juma’a saboda fafutukar da ta ke yi wajen kalubalantar ci gaba da takurawa da kuma dankwafe mata a sassan Iran, ciki har da zanga-zangar da ta jagoranta wadda mata suka rika cire hijabansu don nuna kyama ga tilasta musu da mahukuntan kasar ke yi wajen sanya suturar mai rufe jiki.

Narges Mohammadi, 'yar Iran da ke fafutukar yaki da sanya hijabi da kuma dokar zartas da hukuncin kisa.
Narges Mohammadi, 'yar Iran da ke fafutukar yaki da sanya hijabi da kuma dokar zartas da hukuncin kisa. via REUTERS - MOHAMMADI FAMILY ARCHIVE PHOTOS
Talla

Narges Mohammadi wadda yanzu haka ke tsare a gidan yari, ta samu nasarar lashe kyautar ta Nobel ne bayan jajircewarta wajen jagorantar mabanbantan zanga-zangar adawa da kisan Mahsa Amini matashiyar da ake zargin jami’an tabbatar da da’a na Iran da kashewa bayan kamata da laifin kin sanya Hijabi a bara.

Duk da kamen da aka rika yi a wancan lokaci ‘yar fafutuka kuma ‘yar jarida Narges ta ci gaba da jagorantar gangami, ciki kuwa har da wanda tarin mata suka rika cire hijabansu suna konawa, lamarin da kwamitin bayar da kyautar ta Nobel suka jinjina mata kan yadda ta samar da ‘yanci kin rufe jiki ga tarin matan.

Fiye da shekaru 20 Narges ta shafe ta na wannan fafutuka ta nuna adawa da kyama ga dokar da ta tilasta sanya hijabi da kuma hukuncin kisa, wadanda ke karkashin dokokin Iran, lamarin da ke kaita ga zaman yari a lokuta da dama.

Bayan sanar da sunan Narges a matsayin wadda ta lashe kyautar ta Nobel, shugaban kwamitin bayar da kyautar ta Nobel a Norway Berit Reiss-Andersen ta roki mahukuntan Iran su saki ‘yar fafutuka Narges wadda yanzu haka ke tsare a gidan yari.

Kamu na baya-bayan nan da aka yi wa Narges kuma ta ke ci gaba da tsare a gidan yari shi ne bayan laifinta na kone hijabinta tare da wasu mata 3 a ranar 16 ga watan jiya, wato ranar da aka cika shekara guda da kisan Mahsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.