Isa ga babban shafi

Yau ake cika shekara guda da kisan Mahsa Amini a Iran

Yau asabar ake cika shekara guda da kisan matashiya Mahsa Amini da ake zargin jami’na tsaron tabbatar da da’a na Iran da aikatawa bayan kama ta da laifin kin sanya hijabi.

Shekara guda da kisan matashiya Mahsa Amini.
Shekara guda da kisan matashiya Mahsa Amini. REUTERS - ANUSHREE FADNAVIS
Talla

Wannan kisa dai ya haddasa kakkarfar zanga-zanga a ciki da wajen kasar tare da boren mata wajen kalubalantar ci gaba da bin dokar wajen sanya hijabi da ke matsayin guda cikin dokokin Iran masu karfi da aka kaddamar tun bayan juyin juya halin 1979 da ya mayar da kasar jamhuriyar musulunci.

Don tunawa da zagayowar ranar dubunnan mata sun gudanar da wata zanga-zangar adawa da takurawa mata a sassan Iran musamman a yankin Arewacin kasar da ke matsayin mahaifa ga Amini.

Duk da yadda aka cika shekara guda da wannan kisa, har yanzu Iran na ci gaba da ganin boren jama’a yayinda lamarin ya dawo sabo fil a zukatan ‘yan uwa da tarin kungiyoyin matan da suka jagoranci adawa da kisan matashiyar.

Amini mai shekaru 22 da aka fi sani da Jina, ta yi tattaki ne daga yankin Kurdistan na arewa maso yammacin Iran zuwa birnin Tehran fadar gwamnati gabanin gamuwa da ajalinta a hannun jami’an.

Jim kadan bayan fitar ta daga tashar jiragen kasa ne jami’an tsaron tabbatar da da’ar suka damke ta bisa tuhumar ta da laifin kin saka hijabi.

Tarin kasashen Duniya sun yi tir da wannan kisa tun a wancan lokaci tare da neman bin bahasin musabbabin mutuwar matashiyar baya ga ladabtar da wadanda ke da hannu akai.

Wannan kisa dai ya haddasa wata irin kakkarfar zanga-zanga da kasar bata taba gani ba a tarihi, wanda ya kai ga kone tarin hijabai da mata suka rika cirewa akan tituna don fusata mahukuntan Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.