Isa ga babban shafi

Majalisar dokokin Armenia ta kada kuri'ar amincewa da shiga kotun ICC

Majalisar dokokin Armeniya ta kada kuri'ar shiga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, matakin da ya kara dagula dangantakar kasar da tsohuwar kawarta Rasha, bayan da kotun ta ICC ta bayar da sammacin kama shugaba Vladimir Putin kan abubuwan da ke faruwa a Ukraine.

'Yan majalisar dokokin kasar Armeniya sun halarci zaman majalisar dokokin kasar a birnin Yerevan na kasar.
'Yan majalisar dokokin kasar Armeniya sun halarci zaman majalisar dokokin kasar a birnin Yerevan na kasar. AP - Hayk Baghdasaryan
Talla

A watan da ya gabata gwamnatin Moscow ta kira yunkurin shugaban kasar Yerevan na shiga kotun ta ICC a matsayin rashin aminci, abin da ya sanya ma'aikatar harkokin wajen Rasha gayyatar jakadan Armeniya.

Kasashen da suka rattaba hannu tare da amincewa da yarjejeniyar Rome da ta kafa kotun ta ICC, an basu umarnin su kama Putin idan ya taka kafarsa zuwa kasashen, wanda ake tuhuma da laifukan yaki da ke da alaka da daukar yara daga Ukraine.

Daga baya Armeniya ta tabbatar wa Rasha cewa ba za a hada kai da ita wajen kama Putin ba idan ya shiga kasar.

Mai magana da yawun gwamnatin Kremlin Dmitry Peskov ya kira matakin na ranar Talata da cewa ba daidai ba ne yana mai cewa zai haifar da shakku a Moscow, duk da cewa Armeniya abokiyar huldar kasar ce.

Hukumomin Armeniya sun ce matakin ba shi da alaka da Rasha, sai dai dalilin shigar kasar shine kana bin da suka kira cin zarafi da Azarbaijan ke yi a kasar ne ya tilasta musu shiga ICC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.