Isa ga babban shafi

Azerbaijan: Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Nagorno-Karabakh

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a yankin Stepanakert  da ke Nagorno-Karabakh birni mafi girma a Azerbaijan, domin nuna adawa da katange wuri daya tilo da ya nufi Armeniya.

Masu zanga-zanga kenan da ke dauke da tutar kasar a yankin yerevan
Masu zanga-zanga kenan da ke dauke da tutar kasar a yankin yerevan AFP - KAREN MINASYAN
Talla

Babban dandalin Renaissance na Stepanakert ya cika makil da masu zanga-zanga a ranar Lahadi, inda suka kafa wata babbar tutar Armeniya.

Armeniya da Azabaijan, wadanda ke yaki da juna kan Nagorno-Karabakh da ake takaddama a kai a 2020, a baya-bayan nan suka  sun yi muhawara kan hanyar Lachin.

Kusan makwanni biyu kenan da masu fafutuka na Azerbaijan suka toshe hanyar da ta hada da kasar Armeniya, domin nuna adawa da abin da suke ikirarin hako ma'adinai ba bisa ka'ida ba.

Majalisar dokokin Armeniya ta ce Karabakh na fama da karancin abinci da magunguna da kuma man fetur bayan rufe hanyar da hukumomi suka yi

Sai dai Azerbaijan ta dage cewa babu wani shinge da aka kafa, kuma motocin fararen hula na iya shiga da fita cikin walwala a Karabakh.

Amma Armeniya ta ce dakarun wanzar da zaman lafiya na Rasha da aka tura yankin sun gaza wajen dakile kafa wannan shingen.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, wanda ya yi kira da a sassauta rikicin a ranar Juma'a, ya ce rundunar wanzar da zaman lafiya ta Rasha tana tabbatar da aikinta yayin da take aiki a cikin yanayi mai matukar wahala.

Armeniya da Azabaijan sun gwabza yakin makonni shida a shekara ta 2020.

Fadan dai ya lashe rayukan mutane sama da 6,500 tare da kawo karshen zaman sulhu da Rasha ta yi.

Lokacin da Tarayyar Soviet ta ruguje a shekarar 1991, 'yan awaren Armeniya a Nagorno-Karabakh sun balle daga Azarbaijan, inda rikicin da ya biyo baya kuma ya lakume rayuka kusan mutum 30,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.