Isa ga babban shafi

Tawagar MDD ta samu izinin shiga Nagorno-Karabakh karon farko a shekaru 30

Azerbaijan ta gayyaci jami’an Majalisar Dinkin Duniya don ziyartar yankin Nagorno-Karabakh da nufin ganewa idon su halin da yankin ke ciki, matakin da zuwa bayan ficewar dubunnan Armeniyawan yankin cikin makon da muke bankwana da shi, gayyatar da ke matsayin irinta ta farko da Baku ke mikawa tun bayan tsanantar rikicin bangarorin biyu a shekarar 1990.

Yankin Nagorno-Karabakh na Azerbaijan mai dauke da tsirarun kabilar Armeniyawa.
Yankin Nagorno-Karabakh na Azerbaijan mai dauke da tsirarun kabilar Armeniyawa. AP
Talla

Kakakin Majalisar Stephane Dujarric ya tabbatar da cewa tawagar jami’an za ta ziyarci yankin na Nagorno Karabakh a makon nan, wanda zai zama karon farko da ta ke samun irin wannan dama cikin kusan shekaru 30 da suka gabata, wato tun faro ikirarin Armeniyawan yankin na neman 'yancin kai.

Wannan ziyara dai na zuwa bayan luguden wutar da dakarun Azerbaijan suka yiwa ‘yan awaren yankin tare da kwace makaman da ke hannunsu wanda ya kai ga sallamawarsu a fafutukar da suke game da ‘yancin yankin, inda a yanzu haka kashi 3 bisa 4 na al'ummar yankin suka tsere zuwa Armenia.

A cewar Dujarric Majalisar za ta yi amfani da damar da ta samu ta shiga yankin don duba bukatun da al’umma ke da shi da nufin taimaka musu kama daga wadanda ke ficewa dama wadanda suka yi saura a yankin na Nagorno-Karabakh mai tarihin dadadden rikici tsakanin kasashen Azerbaijan da Armenia.

Majalisar Dinkin Duniyar dai ta bukaci bangarorin su mutunta dokokin kasa da kasa wajen bayar da kariya ga wadanda ke barin yankunansu.

A jawabinsa gaban manema labarai Stephane Dujarric, ya ce abin da zai kai tawagar yankin shi ne bayar da agaji da kuma ayyukan jinkai.

Manyan kasashen Duniya ciki har da Amurka sun mika bukatar ganin Azerbaijan ta bayar da damar kai dauki yankin bayan tsanantar zarge-zargen take hakkin dan adam dama yunkurin shafe kabilar ta Armeniyawa, batun da Baku ke ci gaba da musantawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.