Isa ga babban shafi

Rasha ta ki amincewa da kudirin MDD na tsawaita takunkumi kan Mali

Rasha ta ki kada kuri’a ga kudirin da ya nemi tsawaita ci gaba da zaman jami’an Majalisar Dinkin Duniya da ke sanya idanu kan gwamnatin sojin Mali, kudirin da zai bayar da damar tsawaita takunkuman da majalisar ta kakaba wa kasar tun bayan juyin mulkin Soji.

Wani yanki a Mali.
Wani yanki a Mali. © Moulaye Sayah/AP
Talla

Tawagar jami’an majalisar dai su ke fitar da rahotannin take hakkin dan Adam da ake zargin sojojin kasar da taimakon sojin hayar kamfanin Wagner da aikatawa.

Yayin zaman mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar su 15 a ranar Laraba, Rasha ta hau kujerar na ki game da kudirin wanda ya bukaci tsawaita takunkumin da karin akalla shekara guda baya ga ci gaba da kasancewar jami’an a cikin kasar.

Sai dai Rasha da ke matsayin kawa ga Mali ta yi watsi da wannan kudiri wanda ta ce zai zama karin takura ga kasar ta yammacin Afrika.

Tun farko kasashen Faransa da Hadaddiyar Daular Larabawa suka gabatar da kudirin wanda ya bukaci tsawaita takunkumin shekarar 2017 amma kuma jakadan Rasha Vassily Nebenzia ya kalubalance shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.