Isa ga babban shafi

Nijar ta amince Burkina Faso da Mali su taimaka mata idan aka farmata da yaki

Sojojin da suka kwace mulki a Nijar a watan jiya sun ce za su ba wa sojojin kasashen Burkina Faso da Mali da ke makwabtaka da kasar izinin shiga tsakani a cikin kasar idan an kai musu hari.

Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tchiani tare da mukarrrabansa a birnin Yamai
Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tchiani tare da mukarrrabansa a birnin Yamai © REUTERS/Balima Boureima/File Photo
Talla

Ministocin harkokin wajen Burkina Faso da Mali, Olivia Rouamba da Abdoulaye Diop, sun ziyarci birnin Yamai a ranar Alhamis, inda sabon shugaban Nijar Abdourahamane Tiani ya tarbe su.

Sun yi marhabin da rattaba hannu kan umarnin da ya ba wa sojojin Burkina Faso da Mali izinin shiga tsakani a kan yankin Nijar idan an kai hari, in ji wata sanarwa da mataimakin babban sakataren ma'aikatar harkokin wajen Nijar ya karanta.

Jami’an sojin dai sun hambarar da shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli, lamarin da ya sa kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka ta yi barazanar yin amfani da karfi wajen maido da shi.

Nijar dai ita ce kasa ta hudu a yammacin Afirka tun shekarar 2020 da aka yi wa juyin mulki, bayan Burkina Faso da Guinea da kuma Mali.

Hukumomin mulkin sojan Burkina Faso da Mali sun ce duk wani tsoma bakin soji a makwabciyarsu za su dauke shi a matsayin  ayyana yaki kan kasashensu.

Haka zalika Tiani ya yi gargadi a cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin ranar Asabar da ke cewa: "Idan aka dauki matakin kaddamar da shirin kai hari a Nijar, shakka babu ba zai haifar da ‘da mai ido ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.