Isa ga babban shafi

Shugaban Brazil ya kare alakar da ke tsakanin kungiyar BRICS da Afirka

Shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva ya kare alakar kut-da-kut da kasashen Afirka a lokacin da yake jawabi a taron kasuwanci na BRICS a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu.

Shugaban Brazil Inacio Lula da Silva a taron BRICS
Shugaban Brazil Inacio Lula da Silva a taron BRICS © Imagem: Canal Gov
Talla

Kungiyar BRICS ta kunshi kashen Brazil da Rasha da India da China da Afirka ta Kudu da ke zama manyan kasashe masu tasowa a duniya.

Kasashen biyar na da kashi 40% na yawan al'ummar duniya kuma tana samar da kashi 30% na tattalin arzikin duniya, inda a yanzu haka fiye da kasashe 20 ne suka nemi shiga cikin kungiyar, da  suka hada da Saudiya da Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa.

"Brazil ta dawo nahiyar da bai kamata ta bar ta ba. Afirka na bada damammaki na samun ci gaba, in ji shugaban na Brazil.

"Kungiyar BRICS tana da wata dama ta musamman don tsara yanayin ci gaban duniya. Ya ku ‘yan kasuwa, muna son ku kasance cikin wannan shiri namu. Kasashenmu kadai suna wakiltar kashi 30% na tattalin arzikin duniya."

Tsohon shugaban kasar Jair Bolsonaro bai ziyarci nahiyar Afirka ba a tsawon wa'adin mulkinsa na shekaru hudu.

Shugaban Afrika ta Kudu shi ne mai masaukin baki, inda ya tarbi takwarorinsa na China da Brazil da India. 

Shugabannin kasashen BRICS da suka halarci taron a birnin Johannesburg.
Shugabannin kasashen BRICS da suka halarci taron a birnin Johannesburg. via REUTERS - RUSSIAN FOREIGN MINISTRY

Shugaban Rasha Vladimir Putin bai samu damar halartar taron ba, amma ya tura ministansa na Harkokin Waje domin wakiltar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.