Isa ga babban shafi

Kasashen BRICS na taronsu a Johannesburg

Shugabannin Kungiyar Kasashen BRICS na gudanar da taronsu a Afrika ta Kudu a wannan Talatar a daidai lokacin da suke gogayya da kasashen yammacin duniya da suka mamaye lamurran duniya.

Zauren da shugabannin Kungiyar BRICS ke gudanar da taronsu a Johannesburg na Afrika ta Kudu.
Zauren da shugabannin Kungiyar BRICS ke gudanar da taronsu a Johannesburg na Afrika ta Kudu. AP - Jerome Delay
Talla

Kasashen na BRICS da suka hada da Brazil da Rasha da India da China da Afrika ta Kudu na wakiltar rubu'in kaso na tattalin arzikin duniya, yayin da wasu kasashen suka bayyana sha'awarsu ta shiga cikin kungiyar a baya-bayan nan, wato gabanin soma taronta na kwanaki uku a birnin Johannesburg.

Bayanai na nuni da cewa, akalla kasashen duniya 40 sun sanar da aniyarsu ta shiga cikin kungiyar da suka hada da Saudiya da Bangladesh da Argentina.

An karfafa matakan tsaro a sassan birnin, inda shugaban kasar ta Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya karbi bakwancin takwaransa na China, Xi Jinping da Firaministan India Nerandra Modi da shugaban Brazil Luiz Inacio da Silva da kuma wasu shugabanni akalla 50.

Wani abu da ya dauki hankali shi ne yadda shugaban Rasha Vladimir Putin ya kaurace wa taron na BRICS, inda Ministansa na Harkokin Waje Sergei Lavrov ya wakilce sa.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi wa taron BRICS bayani ta kafar yanar gizo.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi wa taron BRICS bayani ta kafar yanar gizo. AP - Jerome Delay
Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ICC ta bada sammacin cafke shugaba Putin sakamakon zargin sa da aikata laifukan yaki a Ukraine, abin da ake kallo a matsayin babban dalilin da ya hana shi zuwa taron a Johannesburg.

Duk da cewa kasashen na BRICS na wakiltar kashi 40 na yawan al'ummar duniya, amma babu daidaito a bangaren karfin tattalin arzikinsu, inda China ke zama mambar da ta fi karfin tattalin arziki a cikinsu.

Taken tarionsu na bana kuma karo na 15, shi ne "BRICS da Afrika", taron da ke zuwa a daidai lokacin da nahiyar Afrika ta zama dandalin baje gogayyar diflomasiya tsakanin Amurka da Rasha da China da kowacce daga cikinsu ke fafutukar zama mafi karfin fada-a-ji a nahiyar.

Taron ya kuma bayyana karara irin rarrabuwar kawunan da ke tsakanin kasashen duniya dangane da yakin Ukraine, ganin yadda Rasha ke samun goyon bayan mambobin BRICS duk kuwa da matakin da kasashen yamma suka dauka na nuna mata wariya.

Afrika ta Kudu da China da India duk ba su yi Allah-wadai da mamayar Rasha a Ukraine ba, inda kuma Brazil ta ki bin sahun kasashen yamma wajen aike wa Ukraine da makamai, sannan ta ki kakaba wa Rashar takunkumai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.