Isa ga babban shafi

Na isar da sakon gwamnatin sojin Nijar ga Tinubu - Abdulsalam

Jagoran tawagar ECOWAS a Jamhuriyar Nijar, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya ce ya mika rahotonsa kan batutuwan da gwamnatin mulkin soji ta gabatar ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar
Tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar © Daily Trust
Talla

Tsohon janar din ya bayyana fatan cewa, yaki ba zai yi tasiri ba wajen kawo karshen rikicin, yayin da masu ruwa da tsaki ke tunanin samun mafita mai dorewa kan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.

Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya ya yi magana da manema labarai ranar Talata a fadar shugaban kasa da ke Abuja, bayan wani taro da shugaban kasar, wanda shi ne shugaban kungiyar shugabannin kasashen Afirka ta Yamma.

Janar Abubakar, wanda a karshen makon da ya gabata ya yi wata ganawa da hambararren shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum, da shugabannin mulkin soja a kasar, ya ce ya mika wa ECOWAS sharuddan mulkin gwamnatin Abdouramane Tchiani.

Koda aka tambaye shi ko akwai yuwuwar kauce wa daukar matakin soji, sai ya ce “da fatan diflomasiyya ce za ta kawo karshen wannan matsala. Babu wanda yake son yin yaki, ba ya haifar da komai da ya wuce nadama, amma kuma, shugabanninmu sun ce idan aka kasa kuma ba na tsammanin duk za su gaza, amma ina da yakinin za mu isa wani wuri da zai ba mu damar bullewa daga wannan rikici. "

A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar ECOWAS ta bakin kwamishinanta mai kula da harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro, Abdel-Fatau Musah, ta yi watsi da shirin mika mulki ga gwamnatin farar hula a Nijar nan da shekaru uku masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.