Isa ga babban shafi

Kamfanin Wagner na Rasha ya fara daukar sojojin haya a Afirka

Shugaban Kamfanin Sojojin haya na kasar Rasha Yevgeny Prigozhin ya wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna ma'aikatan kamfanin da aka dauka aiki, karon farko tun bayan da ya shirya wani dan gajeren yaki kan jami'an tsaron Rasha.

Yevgeny Prigozhin, chefe do grupo mercenário privado russo Wagner, discursa camuflado e com uma arma nas mãos em uma área deserta em um local desconhecido, nesta imagem estática tirada de um vídeo possivelmente filmado na África e publicado em 21 de agosto de 2023.
Yevgeny Prigozhin, chefe do grupo mercenário privado russo Wagner, discursa camuflado e com uma arma nas mãos em uma área deserta em um local desconhecido, nesta imagem estática tirada de um vídeo possivelmente filmado na África e publicado em 21 de agosto de 2023. via REUTERS - PMC WAGNER
Talla

A cikin faifan bidiyon, shugaban na Wagner mai shekaru 62, ya ce kamfanin na gudanar da bincike da kuma kokarin ganin cewa Rasha ta kasance kan gaba a dukkan nahiyoyi da kuma Afirka.

Muna daukar ma'aikata na gaske kuma muna ci gaba da aiwatar da ayyukan da muka yi alkawarin aiwatarwa," in ji Prigozhin, tare da harba bindigar da ke hannunsa sanye da kayan soja.

Kamfanin Dillacin Labarai na AP ya kasa tantance bidiyon da kansa wanda ya nuna Prigozhin yana tsaye a wani wuri mai launin toka da launin ruwan kasa tare da manyan motocin daukar kaya tare da wasu mutane sanye da kakin soji a nesa kadan da bayansa.

Amma kafafen sada zumunta a Rasha da ke da alaka da shugaban hayar sun ce Prigozhin na daukar ma'aikatan haya a Afirka tare da gayyatar masu saka hannun jari daga Rasha don saka hannun jari a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Kamfanin na Wagner tun daga shekarar 2014, ya fara wanzuwa a fadin Afirka, kuma ana ganin gwamnatin Kremlin na amfani da shi a matsayin wani makami na fadada kasancewar Rasha a Gabas ta Tsakiya da kuma nahiyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.