Faransa ta kawar da sansanoni 226 na bakin haure da ke Paris
Hukumomin Faransa sun fitar da sanarwar cewa yau Talata aka kwashe bakin hauren da aka jibge a sansanoni daban-daban har guda 226 na wucin gadi da aka kafa tun farkon watan Agusta a gaban Otel de Paris da ke Île-de-France.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sanarwar ta ce wannan shi ne karo na 24 da aka gudanar da aikin debe bakin-haure a Ile-de-France tun farkon wannan shekara, inda aka tallafa wa mutane 3,783.
Magajin Garin Birnin Paris ya bukaci a gudanar da aiki don tsugunar da wadannan iyalai da suka zauna a can don tabbatar da cewa, an ba su agajin wurin kwana na gaggawa.
Tun daga farkon watan Agusta, wasu iyalai 12 ne suka yi sansani a kusa da bakin teku, galibi mata masu kananan yara, wadanda sun fito ne daga kasashen Burkina Faso da Cote d'Ivoire da Senegal da kuma Mali.
A ranar Litinin, Magajin Garin Paris ya bukaci a gudanar da wani aiki na tsugunar da wadannan iyalai da suka zauna a can don neman a bada agajin masaukin gaggawa, domin ceto musamman kananan yara da ke da rauni ainun.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu