Isa ga babban shafi

An kashe dan takarar kujerar shugaban kasa yayin yakin neman zabe

Shugaban Ecuador mai barin gado Guillermo Lasso, ya kafa dokar ta baci a daukacin kasar wadda ya ce za ta shafe kwanaki 60 tana aiki, biyo bayan kisan gillar da aka yi wa dan takarar shugabansa Fernando Villavicencio yayin da yake yakin neman zabe a Quito, babban birnin kasar ta Ecuador.

Fernando Villavicencio dan takarar kujerar shugabancin kasar Ecuador jim kadan kafin kisan gillar da aka yi masa yayin neman zabe a birnin Quito
Fernando Villavicencio dan takarar kujerar shugabancin kasar Ecuador jim kadan kafin kisan gillar da aka yi masa yayin neman zabe a birnin Quito REUTERS - KAREN TORO
Talla

An kashe dan takarar mai shekaru 59 ne a ranar Laraba, a dai dai lokacin da ake fusantar matsalar rashin tsaro da tashe tashen hankulan da mahunkuntan Ecuador ke dorawa akan kungiyoyin da ke safarar miyagun kwayoyi.

Kafin mutuwarsa, Villavicencio yayi suna wajen sukar mmasu aikata laifukan cin hanci da rashawa da sauran miyagun laifuka.

Bayanai daga wadanda suka shaida aukuwar lamarin sun ce, sau akalla 30 aka yi harbi kan taron yakin neman zaben da ya gudana a arewacin birnin Quito, inda wani faifan bidiyo ya nuna lokkacin da dan takarar shugaban kasar ke kokarin shiga motarsa don barin wurin, daga bisani kuma aka ji karar harbin bindigogi gami da ihun neman taimako.

A halin yanzu an baza jami’an sojoji a sassan kasar Ecuador cikin shirin ko ta kwana, domin kare rayukan jama’a, wadanda a ranar 20 ga watan Agusta ake sa ran za su kada kuri’unsu a zaben shugabancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.