Isa ga babban shafi

Kasashe 8 sun kaddamar da shirin ceto daji mafi girma a duniya daga tagayyara

Kasashen nahiyar Kudancin Amurka guda takwas sun kaddamar da fara aikin yarjejeniyar hadin gwiwa, domin kare daji mafi girma a duniya wato Amazon da suka yi iyaka da shi.

Dajin Amazon
Dajin Amazon REUTERS - UESLEI MARCELINO
Talla

Shugabannin kasashen sun kuma kalubalanci kasashe masu arziki da su kara jajircewa wajen daukar matakan kawo karshen illar da ake yi wa dajin na Amazon da ke fuskantar barazanar tashin wutar daji wadda a wasu lokuta wasu miyagu ke kunna ta da gangan, sai kuma sare itatuwa.

Brazil ce ta karbi bakuncin taron da ya samu  halartar kasashen Bolivia, Columbia, Ecuador, Peru, Guyana, Suriname da kuma Venezuela.

Daga cikin manyan kudurorin yarjejeniyar da kasashen nahiyar Kudancin Amurkan suka sanya wa hannu akwai, matakin kawo karshen sare itatuwa ba bisa ka’ida ba a  dajin na Amazon mafi girma a duniya nan da zuwa shekarar 203, sai kuma mutunta alkawarin kasar Colombia na dakatar da aikin laluben arzikin man fetur a yankin dajin  da ta yi iyaka da shi.

Bincike ya nuna cewar akalla mutane miliyan 50 ke rayuwa a yankin dajin Amazon, wanda ya kunshi nau’ikan itatuwa da tsirrai da aka kiyasta cewar adadinsu ya kai biliyoyi, abinda ya sanya katafaren dajin taka muhimmiyar rawa wajen rage dumamar yanayi, sakamakon zuke  gurbatacciyar iskar Carbon mai yawan gaske da itatuwan cikinsa ke yi kamar yadda binciken masana kimiyya ya nuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.