Isa ga babban shafi

Sojojin Isra'ila sun kai farmaki a yammacin gabar kogin Jordan

Sojojin Isra'ila sun harbe wani Bafalasdine har lahira tare da raunata akalla wasu mutum hudu, biyu kuma na cikin mummunan hali a birnin Nablus da ke yammacin gabar kogin Jordan, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Falasdinu da kungiyar agaji ta Red Crescent ta sanar.

Wasu Falasdinawa kenan da suka fake a bayan wata mota, a yayin fadan da ake gwabzawa tsakanin sojojin Isra'ila da dakarun Falasdinu a wajen wani asibiti a garin Jenin na Yammacin Kogin Jordan.
Wasu Falasdinawa kenan da suka fake a bayan wata mota, a yayin fadan da ake gwabzawa tsakanin sojojin Isra'ila da dakarun Falasdinu a wajen wani asibiti a garin Jenin na Yammacin Kogin Jordan. AP - Majdi Mohammed
Talla

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce an harbe wani mutum kafin wayewar gari ranar Alhamis, yayin da mayakan Falasdinawa suka ce suna artabu da sojojin Isra'ila da mazauna yankin Nablus.

Akalla Falasdinawa hudu ne suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga, biyu kuma na cikin mawuyacin hali, in ji kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu a wani abin da ta bayyana da arangama da sojojin Isra'ila a gabashin Nablus, wani birni da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan wanda ya kasance cibiyar gwagwarmayar Falasdinawa game da mamayar Isra'ila.

Bataliyar Nablus na dakarun al-Quds Brigades, reshe masu dauke da makamai, ta ce mambobinta suna yakar sojojin mamaya da kungiyoyin da suka kai farmaki a yankin kabarin Yusuf, tana mai nuni da wani wurin ibada a birnin, inda aka sha fama da arangama tsakanin Falasdinawa da sojojin Isra'ila.

Sojojin Isra'ila ba su amsa bukatar jin ta bakinsu ba kan sabon kisan gilla da aka yi wa wani Bafalasdine, wanda ya biyo bayan farmakin da sojojin kasar Isra'ila suka kai a farkon watan nan a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin da ke da nisan kilomita 41, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 12, da jikkata wasu kimanin 100, tare da yin barna mai yawa a kan ababen more rayuwa na farar hula, wanda hakan ya tilastawa dubban mutane tserewa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, sojan Isra'ila daya ya mutu a harin da aka kai yankin Jenin.

A cikin watan Fabrairu ne sojojin Isra'ila suka kashe Falasdinawa 11 tare da raunata fiye da mutane 80 a wani samame da suka kai Nablus wanda ya hada da sojoji 150 da motoci masu sulke da dama. Wannan farmakin ya biyo bayan kasa da wata guda bayan an kashe Falasdinawa 10 a wani hari makamancin haka da aka kai sansanin 'yan gudun hijira na Jenin.

Tashe-tashen hankula a Yammacin Kogin Jordan sun kara tabarbarewa cikin watanni 15 da suka gabata, tare da karuwar hare-haren da Isra'ila ke kaiwa, da kuma hare-haren da Falasdinawa ke kaiwa kan tituna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.