Isa ga babban shafi

Za mu yi amfani da makamai masu kwanso in bukata ta taso- Putin

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi ikirarin cewa kasar ta na da wadatattun makamai masu kwanso da za ta mayar da martini kan Ukraine matukar Kiev ta yi kuskuren amfani da nau’ikan makaman da Amurka ke shirin bata.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha yayin jawabinsa ga manema labarai.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha yayin jawabinsa ga manema labarai. AP - Alexander Kazakov
Talla

A wata zantawar Putin wadda jaridun Rasha suka wallafa a jiya lahadi, shugaban ya ce sam baa bin fargaba ba ne, domin Rasha a shirye ta ke kan nau’ikan makaman na Cluster masu kwanso da ya haddasa cece-kuce.

Tuni dai Ukraine ta fara karbar nau’ikan makaman na Cluster daga Amurka wanda ya haddasa cece-kuce lura da yadda kasashe kusan 100 suka haramta amfani da shi tsawon shekaru saboda hadarinsa, tun bayan da Amurkan ta yi amfani da shi a Iraqi.

Nau’ikan makaman masu kwanso da suka kunshi bama-bama da harsasai na tarwatsewa ne idan an harba su tare da ci gaba da tasiri a yankin da aka yi amfani da su har fiye da shekaru 10 bayan harba su.

A cewar Putin, Rasha a shirye ta ke domin kuwa ta na da mabanbantan nau’ikan makaman masu kwanso da za ta yi amfani da su kan Ukraine idan har kasar ta yi kuskuren amfani da nau’ikan wadanda Amurka ta bata.

Shugaban na Rasha ya bayyana cewa har zuwa yanzu dakarun kasar basu ko shirya amfani da nau’ikan makaman kama daga bom da harsasai ba, duk kuwa da kamfar harsasan da suke fuskanta a fagen daaga amma idan aka kaisu bango ko shakka babu za su fara amfani da shi.

Kungiyar kare hakkin dana dam ta Human Right Watch da kuma dakarun Ukraine sun zargi Rasha da amfani da nau’ikan makaman a baya-bayan nan duk da yadda yarjejeniyar Oslo ta 2008 ta amince da haramta amfani da shi.

Shi kansa matakin Amurka na baiwa Ukraine nau’ikan makaman ya gamu da kakkausar suka daga kungiyoyin kare hakkin dan adam sai dai shugaba Joe Biden y ace basu da zabin da ya wuce bai wa Ukraine makaman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.