Isa ga babban shafi

Sai bayan Ukraine ta fita daga yaki za ta iya zama mamba a NATO - Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya ba da tabbacin cewa Ukraine za ta shiga kawancen sojan NATO, amma hakan ba zai yiwu ba yayin da kasar ke ci gaba da yaki da makwabciyarta Rasha.

Shugaban Amurka Joe Biden kenan, lokacin da yake jawabi a taron NATO da aka shirya a Vilnius na kasar Lithuania, ranar 12 ga watan Yulin 2023.
Shugaban Amurka Joe Biden kenan, lokacin da yake jawabi a taron NATO da aka shirya a Vilnius na kasar Lithuania, ranar 12 ga watan Yulin 2023. © REUTERS / KEVIN LAMARQUE
Talla

Biden ya shaidawa taron manema labarai a kasar Finland kwana guda bayan taron kungiyar inda mambobin kungiyar suka gaza baiwa Ukraine damar shiga NATO, "Ba batun shiga ko akasin haka bane, lokaci ake jira.

Joe Biden ya gana da shugabannin yankin Nordic a Helsinki na kasar Finland, wanda shugaban kasar Sauli Niinisto ya karbi bakuncin taron da ya samu halartar firaministan Sweden, Norway, Denmark da kuma Iceland.

Biden ya jaddada cewa Ukraine za ta zama mamba a kungiyar NATO nan ba da dadewa ba.

Ziyarar da Mista Biden ya kai babban birnin kasar Finland ya kawo karshen rangadin da ya yi a kasashen Turai na kwanaki biyar da aka tsara domin nuna ci gaban da kungiyar tsaro ta NATO ke samu wanda shugaban Amurka ya ce ta karfafa kanta tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.

Finland ta kasance sabuwar memba na kawancen soja a farkon wannan shekarar, shigar da ta ninka iyakar Nato da Rasha sosai.

Biden ya isa Helsinki ne bayan wani taron koli na shekara-shekara da aka gudanar a Vilnius na kasar Lithuania, inda kasashen kungiyar G7 suka amince da tsarin hadin gwiwa na samar da alkawurran tsaro na dogon lokaci ga Ukraine.

Volodymyr Zelensky ya kira sakamakon taron a matsayin gagarumar nasara ta tsaro ga kasarsa amma ya nuna rashin jin dadinsa da Ukraine ta gaza samun abin da take mafarki na shiga NATO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.