Isa ga babban shafi

Finland ta zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO don kalubalantar Rasha

Finland ta zama kasa ta 31 a matsayin mambar kungiyar tsaro ta NATO yau talata, a wani yanayi da ake alakantawa da yakin Rasha a Ukraine zama musabbabin daukar wannan mataki daga kasar wadda a baya ke sahun ‘yan ba ruwanmu.

Shalkwatar kungiyar tsaro ta NATO a Brussels.
Shalkwatar kungiyar tsaro ta NATO a Brussels. AFP - JOHN THYS
Talla

Bayan matakin Rasha na mamayar Ukraine, hakan ya zama babbar barazana ga kasashen Finland da Sweden da ke makwabtaka da kasar lamarin da ya sanya su mika bukatar neman shigarsu kungiyar ta NATO wadda Amurka ke jagoranta.

Tun farko kasashen Turkiya da Hungary suka ki amincewa da matakin shigowar Finland kungiyar ta NATO dalilin da ya jinkirta kasancewarta mamba a kungiyar gabanin sahalewar majalisar Turkiya a makon jiya.

Duk da wannan jan tunga da aka samu, Finland ta zama kasa ta farko da cikin sauri ta samu tikitin shiga NATO tare da mayar da adadin kasashen da ke cikin kungiyar zuwa 31.

Yau talata za a kammala tsare-tsaren da doka ta tanada a shalkwatar kungiyar da ke birnin Brussels inda ministan wajen Finland zai mika takardun tsare-tsaren kasar na shiga kungiyar hade da wasu bayanan tsaro ga sakataren wajen Amurka Antony Blinken, kasar da ke matsayin kula da NATO kuma mafi zuba kudin tafiyar da kungiyar.

A jawabinsa bayan kammala rijistar Finland shugaban kungiyar ta NATO, Jens Stoltenberg ya ce shugaba Vladimir Putin na Rasha ya fara mamayar Ukraine don rage yawan mambobin kungiyar amma sai gashi ya samu sabanin hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.